BARKA DAZUWA HAUSABLAN.COM DOMIN SAMUN SABBIN WAKOKIN HAUSA KOKUMA VIDEO

NOTICE

Sunday, November 8, 2020

Masana antar shirya fina finay nae KANNYWOOD | subada dama akama rahama sadau

 


SUFETO-JANAR na ‘Yansandan Nijeriya, Alhaji Mohammed Adamu, ya ba Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kaduna umarnin ya binciki Rahama Sadau kan iƙirarin da aka yi cewa ta aikata saɓo a kan Manzon Allah (SAW).

Sakamakon wannan umarnin, kwamishinan, Alhaji Umar Muri, ya gayyaci fitacciyar jarumar ta Kannywood da Nollywood da ta gabatar da kan ta a ofishin sa a yau.

Wata ƙwaƙƙwarar majiya da ke kusa da binciken da ‘yansanda ke yi kan wannan magana ta faɗa wa mujallar Fim ɗazu ɗazun nan cewa yanzu haka Rahama ta na kan hanyar ta ta zuwa ofishin kwamishinan daga Abuja.

Majiyar ta ce a da, jarumar ta na kan hanyar ta ne ta zuwa ƙasar Dubai ita da mahaifiyar ta da ƙannen ta uku – Fatima, Aisha da Zainab.

Share With Your Friends:



0 Please Share a Your Opinion.:

About Us | Contact Us |

| Privacy | Promot Music